Afrika-Coronavirus

Afrika na samun nasara a yakin da take yi da annobar coronavirus - WHO

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. 18/5/2020
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. 18/5/2020 Christopher Black/OMS/Handout via Reuters

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhnom Gebreyesus, ya ce ana samu gagarumin cigaba, a kokarin da ake na yaki da annobar COVID-19 a nahiyar Afirka.

Talla

Tedros wanda ke gabatar da taron manema labarai a game da matsayin wannan cuta a duniya, ya ce yanzu haka hukumar na shirin tura karin kayayyakin gwaje-gwaje zuwa nahiyar ta Afirka.

Shugaban hukumar ta WHO y ace a halin da ake ciki kasashen Afrika sun samar da dakunan gwajin cutar coronavirus akalla 51, sabanin karancin wuraren gwajin da nahiyar ta fuskanta a makwannin da suka gabata.

Shugaban hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus kan nasarar da kasashen Afrika ke samu a yaki da coronavirus

Cikin wannan wata na Mayu, Hukumar Lafiya ta Duniya tayi hasashen cewar akalla mutane miliyan 200 annobar coronavirus za ta kama a nahiyar Afirka a cikin shekara guda, yayinda 150,000 za su mutu, muddin hukumomi suka gaza daukar matakan da suka dace wajen dakile annobar.

Binciken kwararrun na hukumar WHO na zuwa ne a daidai lokacin da ake gargadin annobar COVID-19 ta zama babbar barazana ga bangaren lafiya a kasashe masu tasowa, wadanda kawo yanzu ke fafutuka da sauran manyan cutuka sakamakon tabarbarewar fannin lafiyar kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.