Benin

An cafke alkali da kwamishinan ‘yan sanda saboda hada baki da ‘yan ta’adda

Za a gurfanar da babban jami'in kotun Benin gaban kotu bisa tuhumar alaka da ta'addanci.
Za a gurfanar da babban jami'in kotun Benin gaban kotu bisa tuhumar alaka da ta'addanci. Getty Images/Oxford

Jami’an tsaro a Jamhuriyar Benin, sun cafke wani babban jami’in ma’aikatar shari’a da kuma wasu manyan jami’an tsaro uku, bisa zargin rashawa da kuma hada baki da ‘yan ta’adda.

Talla

Tuni dai aka soma shirin gurfanar manyan jami'an a gaban kotu, da suka hada da mai shigarar da karar, kwamishinan 'yan sanda da mataimakansa 2.

An cafke mutanen ne a garin Kandi dake arewacin kasar inda aka kaddamar da bincike a kansu bayan da suka saki wani da ake zargin cewa shi ne ke samar da bayanan sirri ga ‘yan ta’adda, mutumin da aka kama a cikin gandun dajin Parc W dake kan kusurwar kasashen Benin, Nijar da kuma Burkina Faso

Bayan da suka cafke wanda ake zargin, daga bisani jami’an tsaro sun danka shi a hannun mai gabatar da kara na gwamnati da ke garin na Kandi, to sai dai kwanaki kadan aka samu labarin cewa alkalin ya sallami wannan mutum, daga nan kuma sai jami’an tsaro suka mika zance a matakin gaba, lamarin da ya sa aka dakatar da alkalin daga aiki sannan aka cafke shi.

A karkashin dokokin kasar Jamhuriyar Benin, akwai hukuma ta musamman da aka dorawa alhakin hukunta wadanda ake zargi da aikata ta’addanci da ake kira CRIET amma ba wannan alkali ba, dalilan da suka sa ake zargin cewa ga alama ya karbi toshiya ne kafin sallamar wanda ake zargin.

Yanzu haka dai lauyoyi 12 ne suka bayyana aniyarsu ta tsaya wa alkalin da sauran mutane ukun da ake zargi a wannan batu, sai dai kafin bayyana ranar da za a fara yi masu shari’a, tuni lamarin ya dauki hankulan al’ummar kasar ta Benin musamman a kafafen sada zumunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.