Kamaru

Shugaban rediyo da talabijin ya gurfana a kotu sau 30 ba tare da tabbatar da laifinsa ba

Wani lauya a harabar babbar kotun Kamaru dake birnin Yaoundé
Wani lauya a harabar babbar kotun Kamaru dake birnin Yaoundé AFP PHOTO / REINNIER KAZE

An cigaba da shari’ar da ake yi wa Amadou Vamoulke, tsohon shugaban gidan rediyo da talabijin na kasar Kamaru wato CRTV, wanda ake zargi da yin facake da kudaden kafafen yada labaran.

Talla

Shari’ar wadda aka fara a ranar talata, za a ci gaba gudanar da ita har zuwa gobe alhamis, sai dai lauyoyin da ke kare Amadou Vamoulke, sun bukaci a bayar da belinsa saboda dalilai na kare lafiyarsa lura da halin da ake ciki na barazanar cutar COVID-19.

Vamoulke, mai shekaru 70 a duniya, sau 30 yana gurfana a gaban alkali amma ba tare da an tabbatar da laifinsa ba, kuma yanzu haka ya share tsawon shekaru 4 tsare bisa zargin sace kudaden gwamnati.

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare shi, Barrister Alice Nkom, ta ce lura da yadda bangaren shari’a ke tafiyar hawainiya, hakan na kara tabbatar da cewa masu shigar da kara ba su da wasu hujjojin da ke tabbatar da cewa ya aikata laifin da ake zarginsa a kai, saboda haka dole a sake shi.

Bayan share shekaru 4 ana tsare da tsohon shugaban tashar rediyo da talabijin na CRTV, sai a wannan karo ne aka fara gayyatar shaidu domin bayyana abinda suka sani dangane da zargin da ake yi masa, a cewar lauyar dake kare shi Alice Nkom.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.