Afrika

Akinwumi ya yi raddi ga masu tuhumarsa da laifin cin hanci

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina. REUTERS/Thierry Gouegnon

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina ya mayar da martani kan zarge-zargen rashawa da ake yi masa, tare da shan alwashin cigaba da gudanar da aikinsa.

Talla

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina ya caccaki abin da ya kira yunkurin da wasu ke yi na bata masa suna, yayinda ya jaddada aniyarsa ta cigaba da aiki da dukkanin masu ruwa da tsaki.

Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta matsa lamba don ganin an gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Adesina na handame kudade da kuma yi wa makusantansa alfarma.

Adesina wanda ke neman sabon wa’adin shekaru biyar kan kujerar shugabancin bankin na Afrika, ya ce, babu wani laifi da ya aikata, har ta kai wasu na neman zubar masa da kimarsa da mutuncinsa a cewarsa.

Mista Adesina ya kuma bada misali da Nelson Mandela da Koffi Annan, da ya ce rayuwarsu ta nuna cewa, da jibin goshi, Afrika ta bunkasa.

Adesina dai, shi ne mutun na farko daga Najeriya da ya rike wannan mukamin, kuma ya jaddada cewa, muddin za a yi bincike na gaskiya da adalci, to lallai za a same shi ba tare da aikata wani laifi.

Tun da farko dai, Kwamitin Ladabi na Bankin ya wanke Adeshina daga zargin da wasu mafallasa suka yi masa a cikin wata wasika mai shafuka 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.