Najeriya

'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a jihar Sokoto

'yan bindiga a jihar Zamfara a arewacin Najeriya
'yan bindiga a jihar Zamfara a arewacin Najeriya REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

'Yan bindiga sun kai hare-hare a kauyuka da dama a karamar hukumar mulkin Sabon Birni da ke jihar Sokoto jiya Laraba a Najeriya, inda bayanai ke cewa sun kashe mutane akalla 70.

Talla

Bayanai na nuni da cewa ‘yan bindigar masu tarin yawa a kan babura, sun kashe mutane 25 a kauyen Garki, 13 a Dan Aduwa, 25 a Kuzari, 7 a garin Katuma sai kuma 4 wani kauyen mai suna Masawa.

Wadannan hare-hare an kai su ne lokaci kadan bayan da gwamnan jihar ta Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatinsa domin isar da sakon ta’aziya a game da kisan da ‘yan bindigar suka yi wa wasu fararen hula a yankin na Sabon Birni.

An dai jima ana fama da matsalar tsaro a wannan yanki, yayin da jama’a suka kara nuna fargaba tun bayan da rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da farmaki kan maboyar ‘yan bindigar a jihohin Zamfara da Katsina.

Wakilinmu na Sokoto faruk Muhammad Yabo ya aiko da rahoto kan halin da ake ciki.

'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a jihar Sokoto

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.