Burkina Faso

'Yan ta'adda sun halaka 'yan kasuwa 15 a Burkina Faso

Wasu dakarun rundunar sojin kasar Burkina Faso, yayin atasaye.
Wasu dakarun rundunar sojin kasar Burkina Faso, yayin atasaye. MICHELE CATTANI / AFP

Gwamnatin Burkina Faso ta ce ‘yan ta’adda sun halaka akalla mutane 15, yayin wani farmaki da suka kaiwa jerin gwanonin motoci dauke da ‘yan kasuwa a arewacin kasar.

Talla

Sanarwar tace har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na jiya Juma’a, wanda yayin sanadin jikkatar mutane masu yawan gaske, bayaga mutanen da suka mutu, da kuma wadanda har yanzu ba a gansu ba.

Wannan hari na zuwa kwana guda bayan halaka mayakan ‘yan ta’adda 10 da sojin kasar ta Burkina Faso suka yi ranar Alhamis a dai yankin arewacin kasar.

Tun daga shekarar 2017, dakarun sojin Burkina Faso ke fafatawa da mayakan ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyoyin al Qaeda da ISIS, da suka matsa da kai hare-hare a yankunan arewacin kasar.

A cikin watan nan na Mayu, kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta ce akalla makarantun boko dubu 2 da 500 aka rufe daga shekarar 2017 zuwa yanzu, sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda a kasar Burkina Faso.

Kungiyar ta ce sama da dalibai dubu 350 ne suka daina daukar darasi sanadiyyar rufe wadannan makarantu lura da yadda ‘yan bindiga ke afka wa jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI