Afrika

Shugaban bankin Afrika ya sake shiga tsaka mai wuya

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina. Riccardo Savi / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / Getty Images via AF

Bankin Raya Kasashen Afrika ya kaddamar da sabon bincike game da zargin aikata ba daidai ba da ake yi wa shugabansa Akinwumi Adesina dan Najeriya, kwanaki kadan bayan da Amurka ta bukaci a gudanar da binciken. 

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da bankin ke shirin gudanar da zabe a cikin watan Agusta, zaben da Adesina ke fatan lashewa don ci gaba da jagorancin bankin na karin shekaru biyar.

Ana sa ran kammala  sabon binciken kan Adesina nan da  makwanni 4 masu zuwa kamar yadda sanarwar da Majalisar Gwamnonin Bankin ta fitar ta nuna.

A cikin wannan mako ne  shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada goyon-bayansa ga Adesina, domin sake samun wa’adin jagorancin bankin karo na biyu.

Sakamakon binciken farko da aka gudanar kan Adesina, ya wanke shi daga zargin da ake yi masa na handame kudade da kuma yi wa makusantansa alfarma.

Adesina shi ne mutun na farko daga Najeriya da ya dare kan kujerar shugabancin Babban Bankin na Raya Kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI