Faransa

Faransa ta yi ikirarin kashe jagoran Al-Qaeda a Sahel

Jagoran mayakan Al-Qaeda a yankin Sahel, Abdelmalek Droukde.
Jagoran mayakan Al-Qaeda a yankin Sahel, Abdelmalek Droukde. AFP PHOTO/HO

Gwamnatin Faransa ta ce, dakarunta sun kashe jagoran mayakan Al-Qaeda a yankin Maghreb, matakin da ake kallo a matsayin koma-baya ga kungiyar wadda ke kaddamar da munanan hare-hare a sassan yankin Sahel.

Talla

Sanarwar da Ministar Tsaron Faransa, Florence Parley ta fitar a jiya Jumma’a, ta ce, tun a ranar Alhmis da ta gabata, dakarun suka kashe Abdelmalek Droukdel a arewacin Mali, kusa da kan iyakar Algeria, inda kungiyar Al-Qaeda ke da tungarta.

Kungiyar dai ta dauki alhakin kazaman hare-hare da dama da aka kai kan sojoji da fareren hula a Sahel da suka hada da farmakin da ya yi sanadin mutuwar mutane 30, akasarinsu Turawa a wani otel da gidan cin abinci da ke Burkina Faso a shekarar 2016.

Faransa dai ta girke sojoji fiye da dubu 5 domin fatattakar mayakan da ke ikirarin jihadi a yankin Sahel.

Tun a shekarar 2007, wannan kungiya ta Al-Qaeda reshen Maghreb, ta yi mubaya’a ga Osama Bin Laden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI