Libya

Sojojin Libya sun zafafa farmaki kan dakarun Haftar

Wani dauki-ba-dadi a birnin Sirte, mahaifar tsohon shugaban kasar Libya, Mu'ammar Ghaddafi
Wani dauki-ba-dadi a birnin Sirte, mahaifar tsohon shugaban kasar Libya, Mu'ammar Ghaddafi REUTERS/Goran Tomasevic

Dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Libya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, sun zafafa hare-harensu kan sojojin Khalifa Haftar a wannan Lahadi duk da cewa, an samu sassaucin dauki-ba-dadin a wajen birnin Sirte.

Talla

Dakarun na Libya da ke samun goyon bayan Turkiya, sun karbe sauran sansanonin sojin da ke hannun magoya bayan Haftar a yankin yammacin kasar.

Jim kdan da samun koma-baya a karfin sojinsa, Haftar ya garzaya birnin Alkahira na Masar, inda a can ya sanar da aniyarsa ta amincewa da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta wadda shugaba Abdel Fatah al-Sisi ya gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI