Mali

Jagororin zanga-zangar Mali na son sasanta rikicin siyasar kasar

Kungiyar masu zanga zangar adawa da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ta ce wakilan ta sun gudanar da taro da wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na Kungiyar kasashen Afirka AU da kuma na kungiyar ECOWAS domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Masu zanga-zangar adawa da shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali.
Masu zanga-zangar adawa da shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali. REUTERS/Matthieu Rosier
Talla

Majiyar masu zanga zangar ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, wakilan wadannan hukumomi sun bukaci jin korafin da suke da shi da kuma bukatun su na ganin an kawo karshen mulkin Keita wanda ya kasa magance matsalolin da suka addbi kasar.

Mai Magana da yawun dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Olivier Salgado yace shugaban shirin samar da zaman lafiyar Mahamat Saleh Annadif ya gana da wakilan masu zanga zangar tare da wakilan wadannan hukumomi da kuma bangaren gwamnati domin samo maslaha dangane da rikicin kasar.

Rahotanni sun ce cikin wadanda suka halarci taron harda fitaccen malamin addinin Islama Imam Mohammed Dicko wanda a baya ya ke goyan bayan shugaban kasar kafin su raba gari.

Gwamnatin Keita ta ce kofar ta a bude take domin tattaunawa da bangarorin kasar amma kuma dole su mutunta bangarorin dimokiradiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI