Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram dubu 1 da 429 a kwana 60

Ganawar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da babban hafson Sojin Kasar Yusuf Buratai.
Ganawar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da babban hafson Sojin Kasar Yusuf Buratai. Solacebase

Babban Hafson Sojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai ya ce a cikin kwanaki 60 da ya yi yana jagorancin dakarun sa wajen yaki da mayakan kungiyar boko haram a yankin arewa maso gabas, sojojin sun kashe mutane 1,429 bayan kama wasu 116 da ake zargin suna taimakawa yan ta’addan.

Talla

Yayin da ya ke jawabi ga manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Janar Buratai ya ce shugaban ya yaba da nasarar da suka samu, yayin da sojojin ke cigaba da sadaukar da rayukan su domin murkushe mayakan.

Janar Buratai ya yabawa rawar da jami’an leken asirin sojin da na hukumar DSS da kuma Civilian JTF suke bayarwa wanda ya kaiga samun gagarumar nasara.

Hafsan sojin ya ce ko a lokacin da yake fagen daga, ana cigaba da yiwa shugaban kasa bayani akai akai kan yadda al’amura ke gudana wajen yakin da suke, yayin da dakarun suka sake samun karfin gwuiwar cigaba da yakin.

Janar Buratai ya ce zai cigaba da zuwa bakin dagar domin jagorancin dakarun sa, yayin da yayi alkawarin cewar suma sauran yankunan dake fuskantar tsaro musamman na arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya ba za’a bar su a bay aba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI