Sudan ta Kudu

Tsagin 'yan tawayen Sudan ta kudu zai kalubalanci gwamnati

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu da mataimakinsa Riek Machar kuma tsohon madugun 'yan tawayen Kasar.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu da mataimakinsa Riek Machar kuma tsohon madugun 'yan tawayen Kasar. REUTERS/Jok Solomun

Fitaccen dan kasuwar Sudan ta kudu kuma tsohon babban jami’in sashen fikira na kasar Kebino Wol ya sha alwashin hambarar da gwamnatin shugaba Salva Kiir daga mulki ta hanyar kafa sabuwar kungiyar ‘yan tawaye da za ta kalubalanci gwamnati.

Talla

Mr Wol wanda ke cikin tawagar ‘yan tawayen da shugaba Salva Kiir ya yiwa yafiya a watan Janairu ya ce tuni ya kafa kakkarfar kungiyan mayakan ‘yan tawaye da za ta kalubalanci gwamnatin kasar mai cike da rashawa da nuna banbanci.

Kawo yanzu dai gwamnatin Sudan ta kudu ba ta mayar da martani kan ikirarin Kerbino Wol da ya ayyana kansa a matsayin sabon madugun ‘yan tawaye ba.

Duk da matakin kafa gwamnatin hadaka a Sudan ta Kudu watanni 6 da suka gabata, har yanzu an gaza samun haduwar kai tsakanin mabanbantan kabilu inda ko a baya-bayan Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yadda rayukan dubunnan fararen hula suka salwanta a rikicin kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.