Najeriya-Kano

Kashi 60 na mace-macen Kano Coronavirus ce -rahoto

Ma’aikatar Lafiya a Najeriya ta bayyana cewa, kashi 60 cikin dari na mace-macen da jihar Kano da ke arewacin kasar ta fuskanta watanni biyu da suka gabata sun mutu ne sanadiyyar cutar coronavirus.

Guda cikin cibiyoyin kula da masu Coronavirus a Jihar Kano ta arewacin Najeriya.
Guda cikin cibiyoyin kula da masu Coronavirus a Jihar Kano ta arewacin Najeriya. RFI Hausa / Abubakar Dangambo
Talla

Tun bayan rahoton mutuwar fitattun mutane 150 cikin kankanin lokaci a jihar da jaridun Najeriyar suka wallafa a watan Aprilu, kwamitin da ke yaki da COVID-19 karkashin sakataren gwamnatin kasar ya aike da tawagar kwararru na musamman da nufin gudanar da bincike kan batun.

Sai dai rahoton kwamitin da kwamitin ya fitar jiya Litinin, ta bakin ministan lafiyar kasar Osagie Ehanire ya bayyana cewa mutum 979 da suka mutu a wancan dan tsakanin cikin kananan hukumomin jihar 8 na tsakar birni na da cikakkiyar alaka da COVID-19.

Cikin watan na Aprilu dai jihar Kano wadda bisa al’ada ke samun alkaluman mutum 11 kowacce rana a kananan hukumomin 8, a wancan lokaci ta rika samun mutuwar mutum 43 a kowacce rana, ko da dai mahukuntan jihar sun nesanta yawaitar mace-macen da coronavirus.

A jawabin da Ehanire ya gabatar ya ce tababs bincikensu ya nuna kashi 50 zuwa 60 na mace-macen a jihar Kano ya faru ne sanadiyyar Coronavirus wadda yanzu haka ta kama mutum fiye da dubu guda a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI