Sojin Faransa 2 sun jikkata yayin kuskuren harbi a fadar shugaban Chadi
Rundunar Sojin Faransa ta ce sojinta biyu da ke Chadi sun samu rauni lokacin da dakarun tsaron fadar shugaban kasa Idris Deby suka bude musu wuta a N’Djamena a matakin da aka bayyana shi a matsayin kuskure.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kanar Frederic Barbry, mai Magana da yawun sojin, ya ce sojojin biyu na sintiri ne a fadar shugaban kasar domin shirya wata ziyara lokacin da aka samu hadarin, ba tare da karin bayani kan dalilin da ya haifar da harbin da ya jikkata su ba.
Jami’in ya ce sojojin basa cikin hadari, kuma an dauke su daga fadar shugaban inda aka samu hadarin.
Wani soja daga cikin masu tsaron fadar shugaba Deby ya ce sojin Faransa da basa sanye kayan soji sun isa fadar shugaban kasar ne a wata mota jeep kirar Prado, inda suka tsaya a kofar shiga, abinda ya sa masu tsaron fadar suka bude musu wuta, kafin daga bisani wata mota ta je ta dauke su.
Shugaba Idris Deby da ya kwashe sama da shekaru 30 a karagar mulki, na daya daga cikin abokan huldar Faransa, kuma dakarun sa na daga cikin wadanda suka yi fice a yankin.
Dakarun Chadi na daga cikin tawagar sojojin dake aiki a rundunar G5 Sahel dake yaki da yan ta’adda a Mali daga cikin sojoji 5,000 da suka fito daga kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da Mauritania wadanda ke aiki tare da rundunar Barkhane ta sojin Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu