Burundi

Takaitaccen tarihin marigayi shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi

Tsohon shugaban Burundi Pierre Nkurunziza.
Tsohon shugaban Burundi Pierre Nkurunziza. REUTERS/Evrard Ngendakumana

Da tsakar ranar yau Talata ne, fadar shugaban kasar Burundi ta tabbatar da mutuwar Shugaba Pierre Nkurunziza bayan fama da bugun zuciya. Mutuwar shugaban wanda ke mulki Burundi tun daga shekarar 2005 na zuwa ne bayan zaben watan jiya da jam'iyyarsa ta samu gagarumin rinjaye.

Talla

Nkurunziza wanda masu rajin tabbatar da Demokradiyya ke kallon mulkinshi a matsayin na kama karya, musamman bayan tababar da ta biyo bayan rikicin siyasar 2015 da ya bashi damar ci gaba da zama kan karagar mulki a zagaye na 3, bayanai sun nuna an haifeshi ranar 8 ga watan Disamban 1964 wanda ke nuna ya mutu yana da shekaru 55 a duniya.

An dai haifi Nkurunziza a wani gari mai suna Ngozi da ke cikin birnin Bujumbura a yankin arewacin kasar, Mahaifin Nkurunziza mai suna Eustache Ngabisha, dan kabilar Hutu ne da ya fito daga gidan Sarauta yayinda mahaifiyarsa ta fito daga kabilar Tutsi.

Za a iya cewa Nkurunziza ya fara koyon salon siyasa daga mahaifinsa Ngabisha wanda da shi aka yi gwagwarmayar kwato ‘yancin kasar gabanin zabensa a matsayin dan Majalisar dokoki yayinda daga bisani ya zama gwamnan yankunan kasar 2 kafin kisanshi a shekarar 1972.

Nkurunziza ya yi karatunsa daga matakin Firamare zuwa digiri a cikin kasar ta Burundi, inda ya kammala digirinsa a bangaren ilimin wasanni a shekarar 1990 gabanin barkewar yakin basasan kasar.

A shekarar 1995 ne Nkurunziza ya fada harkokin siyasa inda ya wakilci dubun-dubatar matasan kabilar Hutu bayan kisan daruruwan dalibai ‘yan kabilar a wani rikici inda kai tsaye ya dare matsayin mataimakin babban sakataren Jam’iyyar ta CNDD-FDD gabanin zama shugaban Jam’iyyar dungurugum a shekarar 2001 aka kuma sake zabarsa a 2004.

A watan Yunin 2005 ne Nkurunziza ya lashe zaben kasar inda aka rantsar da shi ranar 26 ga watan Agustan shekarar, tun daga nan ne yak e mulkin kasar har zuwa mutuwarsa a jiya Litinin 8 ga watan Yunin 2020.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.