Amnesty ta zargi sojojin Sahel da kissan gilla

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi dakarun sojin dake aiki a Yankin Sahel da kisan gilla da kuma batar da mutane akalla 200 a cikin wannan shekara wanda ake iya danganta shi da laifuffukan yaki.

Sojojin Mali yayin gudanar da atisaye a yankin Sahel
Sojojin Mali yayin gudanar da atisaye a yankin Sahel AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES
Talla

Kungiyar tace sojojin kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar sun kasha akalla fararen hula 57 a cikin wannan shekara, yayin da 142 suka bata tsakanin watan Fabarairu zuwa Afrilun da ya gabata.

Akasarin yankunan Sahel sun fada cikin tashin hankali sakamakon yawan Yan bindigar dake dauke da makamai suna kai hare hare kan fararen hula tun bayan barkewar tashin hankali a kasar Mali a shekarar 2012 wanda ya bazu zuwa cikin kasashen Burkina Faso da Nijar.

Duk da kasancewar dakarun rundunar Faransa da ake kira Barkhane a Yankin da kuma na Majalisar Dinkin Duniya, sojojin kasashen Yankin na cigaba da fafatwa domin kare jama’ar kasashen su.

Dubban sojoji da fararen hula sun yi asarar rayukan su a wannan tashin hankali, yayin da wasu kuma suka tsere daga muhallin su domin tsira da rayukan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI