Coronavirus

Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Duniya

Jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji saman wani marasa lafiya
Jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji saman wani marasa lafiya Reuters/Afolabi Sotunde

Adadin Mutanen da annobar coronavirus ta kama a Duniya ya zarce miliyan 7, yayin da sama da miliyan 3 suka warke, kana sama da 400 suka mutu.

Talla

Alkaluman hukumar lafiya ta duniya sun nuna cewar ya zuwa daren jiya, mutane miliyan 7 da dubu 169 da 550 suka harbu da annobar COVID-19, kuma miliyan 3 da dubu 148 da 200 sun warke, yayin da dubu 407 da 914 suka mutu.

Har yanzu Amurka ke sahun gaba wajen samun wadanda suka mutu, inda suka kai dubu 111 da 375, sai Birtaniya mai mutane sama da dubu 40, sannan Brazil mai 37,134 sai italia mai mutane 34,043 sannan Faransa mai mutane 29,296.

A nahiyar Turai kawai annobar ta kasha mutane 184,807, sai Amurka da Canada mai dauke da mutane 119,316, yayin da Afirka ke da 5,512.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI