Tsoffin 'yan wasan Afirka sun bi sahun yaki da coronavirus

Tsohon Kaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya Super Eagles
Tsohon Kaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya Super Eagles REUTERS/Michael Dalder/File Photo

Tsoffin fitattun 'Yan wasan kwallon kafar Afirka sun shiga gasa a kafofin sada zumanta na Intanet, a kokarin da suke na wayar da kan jama'a game da yadda za a taimaka a hana yaduwar cutar Korona.

Talla

Tsoffin fitattun 'yan wasan kwallon kafa na kasa da kasa da suka hada da Ahmed Hassan na Masar, Joseph Yobo na Najeriya, Karim Haggui na Tunisiya da Lomana LuaLua na Congo sun shiga cikin wannan shirin.

'Yan wasan suna nadan faya-fayan bidiyon daban-daban inda suke kira ga al’umma yadda za’a gujewa kamuwa da annobar Korona, a wani bangare na Kamfen din « Afrika ta kasance cikin lafiya »

Yanzu haka dai COVID – 19 ta haddasa rasa rayukan mutane sama da dubu 5 a Nahiyar Afirka cikin sama da dubu 200 da aka tabbatar suna dauke da ita.

Mataimakin sakatare-janar na hukumar kwallon kafar Afirka, Anthony Baffoe ya ce "Kwallon kafa na hada mutane da yawa dake da asali daban-daban da kabila ko yare, don haka suke fatan wannan shiri ta kafafofin sada zumunta yanar gizo, ya hada mutane wuri guda, tare da yaki da wannan annoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI