Najeriya

'Yan Boko Haram sun halaka sojoji da mazauna yankin Gubio

Mayakan boko da suka gwabza fada da sojojin Najeriya
Mayakan boko da suka gwabza fada da sojojin Najeriya Defencepost

Mayakan Boko Haram sun kai hari kauyen Felo dake yankin Gubio a Jihar Barno, inda suka kashe mutane akalla 59. 

Talla

Mayakan sun kai harin ne a ranar Talata da rana, inda suka dinga bude wuta kan mazauna kauyen dake gudu, yayin da wasu kuma suka banke su da mota.

Babakura Kolo, wani mazaunin kauyen yace harin kamar ramako ne, ganin yadda mazauna kauyen suka kafa kungiya domin hana mayakan dake zuwa suna sace musu dabbobi.

Gubio na da nisan kilomita 80 daga Maiduguri. Ko a karshen mako mayakan boko haram sun kai hari kan dakarun Najeriya inda suka kasha 6 daga cikin su, yayin da sama da 40 suka bata.

Lamarin rashin tsaro na ci gaba da ciwa da dama daga cikin mazauna kauyuka a Najeriya tuwo a kwariya,yayinda gwamnati ke jaddada cewa ta na iya kokarin ta don kawo karshen yan kungiyar Boko haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.