Harin ta'addanci ya kasashe akalla sojoji Cote d'Ivoire 10

Majisar Tsaron kasar Ivory Coast tace, wasu da ake zaton maharan jihadi ne, sun kai farmaki sansanin sojin kasar dake iyaka da Burkina Faso, cikin daren Laraba wayewan Alhamis, inda suka kashe akalla jami'an saro 10.

Sojin Cote d'Ivoire rike makamin roka a Bouake.
Sojin Cote d'Ivoire rike makamin roka a Bouake. Photo: Issouf Sanogo/AFP
Talla

Wannan dai shine karon farko da mayaka maso ikirarin jihadi suka kaddamar da farmaki cikin kasar Cote’Ivoire tun bayan harin watan Maris na shakarar 2016, a wani wurin shakatawa a gabar tekun Grand – Bassam da ya hallaka mutane 19.

Majiyoyin tsaron Burkina Faso sunce, harin da aka kisa shi kan sansanin kan iyaka dake Kafolo, ya hallaka sojoji 10 da jandarma daya, yayin da wasu 6 suka jikkata kana wasu biyu suka batce.

Sai dai wata majiyar Cote’Ivoire kuma tace mutane 10 aka kashe ciki harda maharani, sai kuma biyu da suka batce.

Masana harkokin tsaro sun dade da nuna damuwa kan yadda mayakan jihadi da suka bulla a Mali a shakarar 2012, dake zafafa hare-haren a yankin Sahel ka iya bazuwa kasashen tekun Guinea.

Kasar Cote’Ivoire dai ta na dokan iyaka da ya kai kilomita 550 da Burkina Faso da ‘yan ta’adda sukayi kaka gida da kaddamar da munanan hare-hare da ya hallaka kusan dubu 1, kana ya raba sama da mutane dubu 860 daga gidajensu cikin shekaru biyar da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI