Ni zan binne abokan gaba na - Alpha Conde

Shugaban Guinea Konakry Alpha Conde
Shugaban Guinea Konakry Alpha Conde WU HONG / POOL / AFP

Shugaban Kasar Guinea Alpha Conde ya yi watsi da rade radin da ake cewa bashi da lafiya, inda yake cewa lafiyar sa kalau kuma zai cigaba da rayuwa har sai ya binne abokan gaban sa da dama.

Talla

Conde mai shekaru 82 ya shaidawa gidan rediyon Sabari FM cewar likitoci suka bukaci takaita bayyana a jama’a da kuma karbar baki saboda annobar coronavirus, amma shi yana cikin halin lafiya.

Shugaban ya shaidawa yan kasar Guinea cewar yana nan lafiyar sa kalua, kuma zai cigaba da wasannin motsa jiki domin kare lafiyar sa.

Annobar COVID-19 ta kashe mutane da dama cikin su harda manyan jami’an gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI