Tubabbun Mayakan Boko Haram 603 za su koma cikin jama'a
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Najeriya ta ce ta na shirin sakin tubabbun mayakan boko haram 603 da aka sauyawa tunani zuwa cikin jama’ar da suka fito daga watan Yuli mai kamawa bayan an kammala sauya musu tunani da kuma horar da su sana’oi.
Ma’aikatar tsaron Najeriya ta sanar da wannan shiri na sallamar tubabbun mayakan boko haram 603 da ake horar da su aka kuma sake musu tunani domin wasti da hanyar da suka kama.
Babban jami’in yada labaran ma’aikatar Manjo Janar John Enenche ya sanar da shirin yayin da ya ke gabatar da ayyukan da dakarun kasar ke yi da kuma irin nasarorin da suke samu.
Janar Enenche ya ce cibiyar horar da tubabbun mayakan ta karbi mutane 893 kuma 280 daga cikin su wadanda suka hada da 'yan kasar chadi biyu sun kamala samun horo kuma an mayar da su cikin jama’a ta hannun hukumomin kasashen su.
Jami’in ya ce yanzu haka akwai mutane 603 da ke samun horo kuma ana saran za su kamala samun horar a watan gobe inda ake saran sallamar su.
Janar Enenche ya ce ana kula da tsoffin mayakan kamar yadda dokokin duniya suka tanada, inda jami’ai 468 daga kungiyoyi daban daban guda 17 cikin su har da jami’an tsaro ke aikin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu