Idris Deby ya kori Janar din sojan kasar

Shugaban Chadi Idriss Deby Itno sanye da kakin soji a fagen-daga da Boko Haram
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno sanye da kakin soji a fagen-daga da Boko Haram prnigeria

Gwamnatin Kasar chadi ta kori daya daga cikin Janar Janar na sojin kasar, Ahmat Koussou Moursal bayan ya rubuta wasika yana sukar shugaban kasa Idris Deby.

Talla

Sanarwar gwamnatin kasar yace Janar Moursal ba zai karbi ko sisin kwabo ba a matsayin kudin ritaya ko sallama daga aiki bayan ya kwashe shekaru da dama yana yiwa kasar aiki.

Janar Moursal ya zargi shugaba Deby ne da kauda kan sa daga tsoffin abokan aikin sa dake Guera da kuma kin biyan diyya ga mutanen da tsohon shugaban kasa Hissene Habre yaci zarafin su.

'Yan adawa a kasar Chadi dai na zargin shugaban Idris Deby Itno, da ya karbi mulki ta hanyar tawaye da neman dawwama kan madufun iko ta hanyar kawar da duk abin da ka zama barazana ga mukaminsa.

Kungiyoyin tawaye na kokarin sun kawar da shi kamar yadda aka saba a siyasar kasar, to sai dai Deby na samun goyon bayan Faransa dake kara shi.

Ko watan Fabarairun 2019, sai dai jiragen yakin Faransa suka ragargaza wata katafariyar tawagar mayakan ‘yan tawaye da suka yi yunkuri ketara kan iyakar kasar ta Chadi daga Libya.

Shugaba Deby da kansa ya bayyana haka  yayin jagorantar taron majalisar zartaswar kasar, inda ya ce ba a samu hasarar ran ko da sojan kasar guda ba, da ke taimakawa dakarun na Faransa.

A cewar Deby, bayan shafe kwanaki uku suna kaiwa ‘yan tawayen farmaki, jiragen yakin Faransa sun yi nasarar tarwatsa motocin yaki 20 daga cikin 50 da mayakan ‘yan tawayen suka yi yunkurin kutsawa cikin kasar ta Chadi da su.

Sai dai kakakin kungiyar mayakan ‘yan tawayen na UFR Yousouff Hamid ya musanta Ikirarin na shugaba Deby, inda ya ce sun yi nasarar kutsawa cikin kasar ta Chadi.

A watan Janairu na shekarar 2009 kungiyoyin ‘yan tawayen takwas na kasar Chadi suka hada gwiwa wajen kafa kungiyar ta UFR da nufin hambarar da gwamnatin shugaba Idris Deby, wanda ya dare shugabancin kasar a 1990 bayan hambarar da tsohon shugaba Hissene Habre.

A shekarar 2008 wasu kungiyoyin ‘yan tawayen Chadi uku da suka taso daga gabashin kasar, sun yi nasarar kutsawa har zuwa gaf da fadar shugaban kasa, kafin daga bisani sojin kasar su yi nasarar watsa su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI