Nijar

RSF da kungiyoyin 'yan jaridu 30 sun yi tir da tsare 'yar jarida a Nijar

Wasu kungiyoyin ‘yan jaridun 30 a Jamhuriyar Nijar, tare da Kungiyar ‘yan jaridu ta Duniya Reporters without Borders (RSF), sun tir da matakin gwamnati na garkame wata ‘yar jiridar kasar Samira Sabou, da ake zargi kage cikin labarin da ta wallafa dangane da badakalar cikinikin makamai a kasar.

Shugaban kungiyar RSF reshen Afrika Assane Diagne Arnaud Froger da jami'an kungiyar a Senegal.
Shugaban kungiyar RSF reshen Afrika Assane Diagne Arnaud Froger da jami'an kungiyar a Senegal. RFI / William de Lesseux
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar Alhamis din nan, La Maison de la Presse, wanda ta hada kungiyoyin 'yan jaridun Jamhuriyar Nijar 30, ta bayyana takaicin ta da matakin na tsare Samira Sabou.

A bangare guda itama kungiyar kare ‘yancin ‘yan jaridu ta duniya RSF, ta bi sahun kungiyoyin na Nijar wajen sukar matakin, inda shugaban kungiyar da ke kula da sashin Afirka Arnaud Froger, ke cewa tsare ‘yar jaridar kan aikinta ya saba dokokin duniya, tare da mika bukatar gaggauta sakinta daga gidan yarin da ta ke tsare yanzu haka.

A Larabar da ta gabata ne gwamnatin Nijar ta tsare ‘yar jaridar Samira wadda ta yi kaurin suna wajen tonon silili a shafinta na Intanet, kamen da ke biyo bayan karar da dan shugaban kasar kuma mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Sani Mahamadou Issoufou ya shigar yana zarginta da bata masa suna, kamar yadda makusantar ‘yar jaridar suka wallafa a shafukan sada zumunta.

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, ‘yar jaridar ta wallafa wani labari ranar 26 ga watan Mayun da ya gabata inda cikin labarin ta ke zargin wani dan kasuwa da ke matsayin abokin dan shugaban kasar, da karban kwangilar sayen makamai daga ma'aikatar staron kasar da sunan dan shugaban.

Tuni dai wannan zargi ke ci gaba da haddasa cecekuce a Jamhuriyyar Nijar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI