Afrika

Kasashen Afrika 54 sun bukaci MDD ta gudanar da mahawar kan Kabilanci

A yayin da ake ci gaba da zanga zangar nuna kyamar kabilanci bayan kisan gillar da yan sanda Farar Fata su ka yi wa George Floyd bakar fata a Amruka.Kasashen Afrika, sun bukaci hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya da ta gudanar da Mahawarar gaggawa kan kabilanci da kuma nuna rashin imanin da yan sanda ke yi.

Fotografia de família da União Aficana (ministra guineense Suzi Barbosa de azul no centro) em Addis Abeba a 9 de Fevereiro de 2020.
Fotografia de família da União Aficana (ministra guineense Suzi Barbosa de azul no centro) em Addis Abeba a 9 de Fevereiro de 2020. RFI/Miguel Martins
Talla

A cikin wata wasika a madadin gungun kasashen nahiyar Afrika 54 kan batutuwan da suka shafi kare hakkin dan adam, da ya aikawa hukumar dake kula kare hakkin dan adam taq duniya.

Jikada Burkina Faso a Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci hukumar kare hakkin dana dam ta MDD, ta gaggauta gudanar da mahawara kan shi’anin da ya shafi nau’oin nuna wariya da kalibanci, tare da mummunar dabi’ar nuna rashin imanin da yan sanda ke yi kan masu zanga zangar lumana.

Sai dai kuma, a yayin da duniya ke bayyana bacin ranta kan batun na nuna rashin imanin  yan sanda kan bakar Fata a Amruka, shugaban kasar Donald Trump ya ce  a wani lokaci ya na da matukar muhimmanci 'yan Sanda su makure wuyar wanda suke zargi da aikata laifi, wanda hakan ke nuna rashin damuwar shugaban daga duk wata sukar matakin da duniya ke yi a halin yanzu, sakamakon kisan gillar da aka yi wa George Floyd, da ya haifar da zanga zanga a ciki da wajen Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI