Turai

Kasashen Turai sun amincewa Astrazeneca domin samar da maganin Coronavirus

Wasu daga cikin magungunan da kamfanin Astrazeneca ke samar da su  a kasuwanin Duniya
Wasu daga cikin magungunan da kamfanin Astrazeneca ke samar da su a kasuwanin Duniya REUTERS/Stefan Wermuth

Kasashen Faransa da Italia da Jamus da Netherlands sun sanya hannu a kan yarjejeniya da kamfanin hada magungunan Astrazeneca domin samar musu da maganin rigakafin kamuwa da cutar coronavirus.

Talla

Ministan lafiyar Italia Roberto Speranza yace kwangilar ta kunshi samar da kwalabai miliyan 400 na maganin wanda kamfanin ya samar tare da Jami’ar Oxford wanda tuni aka yi nisa wajen tantance sahihancin sa.

Sparanza yace kasashen 4 na saran karbar kashi na farko na maganin nan da karshen wannan shekara.

Majalisar gudanarwar kungiyar kasashen Turai tace ta samu izini daga gwamnatocin kasashen dake yankin da ta tattauna shirin sayen maganin domin raba su a sauran kasashen dake nahiyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI