Mayakan boko haram sun sake kaddamar da hari a Jihar Barnon Najeriya
Wasu Yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan boko haram ne sun kaddamar da hare hare yau da rana a kananan hukumomi 2 dake Jihar Barnon Najeriya.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce mayakan dauke da muggan makamai sun kai harin ne a garin Manguno da misalin karfe 11.30 na safiyar yau inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, yayin da sojoji suka mayar da martani.
Wani jami’in kungiyar agaji a garin ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar garin ya kaure da karan harbin bindiga a musayar wutar dake gudana tsakanin mayakan da jami’an tsaro.
Yayin da ake wannan fafatawar, rahotanni sun ce wasu maharan sun kuma kai hari kauyen Usmanati Goni dake karamar hukumar Nganzai yau da safe.
Wadannan hare hare na zuwa ne kwanaki bayan kazamin harin da mayakan suka kai Gubio inda suka kashe fararen hula 81 suka kuma sace mutane 6 da daruruwan dabbobi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu