Najeriya

Yan bindiga sun sake kashe wani Basarake a Katsina

Daya daga cikin jami'an tsaro a wani kauyen jihar Katsina dake Najeriya
Daya daga cikin jami'an tsaro a wani kauyen jihar Katsina dake Najeriya PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Yan bindigar da suke kai hare hare a Jihar Katsinan Najeriya ba tare da kaukautawa ba sun sake kashe wani Basarake da ake kira Sarkin Fulanin Fafu, Alh Dikko Usman dake kauyen Mazoji daren jiya juma'a.

Talla

Kisan basaraken  na zuwa ne kwanaki bayan irin wanda aka yiwa Hakimin Yantumaki Atiku Maidabino a fadar sa dake Yantumaki a karamar hukumar Danmusa abinda ya haifar da zanga zangar matasa da kuma tare hanya domin nuna bacin ran su da abinda suka kira watsi da su da gwamnati tayi wajen kare lafiyar su.

Rahotanni sun ce Yan bindigar sun kai harin ne har zuwa gidan Basaraken dake karamar hukumar Matazu inda suka hallaka shi.

Matsallar tsaro a Jihar Katsina ta dada tabarbarewa inda Yan bindiga da rana ke yawo kan Babura suna kai hare hare kauyuka da garuruwa ba tare da jin tsoro ba.

Al’ummar Jihar da Yan Najeriya da dama ne ke sukar gwamnatin tarayya kan yadda ta kasa shawo kan wannan al’amari na rashin tsaro wanda ya baiwa Yan bindigar damar cin karen su babu babbaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.