Najeriya

Yan Sanda a Najeriya sun tsare masu tsaron lafiyar Aisha Buhari

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari tayi zargin cewar hukumar Yan Sandan kasar ta tsare jami’an kula da lafiyar ta sakamakon zargin harbi da bindiga a fadar shugaban kasa.

Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari
Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari TWITTER/AISHA M. BUHARI
Talla

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar daren jiya juma’a Uwargidan shugaban kasar ta aike da sako ta kafar twitter inda ta bukaci Sufeto Janar na Yan Sanda da ya saki jami’an na ta domin kaucewa jefa rayuwar su cikin hadari.

Binciken jaridar yace babban dogarin Aisha Buhari Usman Shugaba da babban jami’in dake samar da tsaro a tawagar Yan sandan dake kare lafiyar ta na daga cikin wadanda aka tsare.

Jaridar tace tsare mutane ta biyo bayan wata matsala da aka samu tsakanin Uwargidan shugaban da wani jami’in shugaban kasa da ya koma Abuja daga Lagos yaki yarda ya killace kan sa a matsayin kariya daga cutar coronavirus.

Premium times tace yayin takaddama tsakanin Uwargidan shugaban kasar da hadimin shugaban ya sa jami’an Yan Sandan suka yi harbi da bindiga wanda hakan laifi ne.

Aliyu Abdullahi, mai baiwa Aisha Buhari shawara kan harkokin yada labarai ya tabbatarwa Jaridar kama jami’an.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI