Afrika

Dakarun wanzar da zaman lafiya biyu a Mali sun mutu

Wasu Yan bindiga a kasar Mali sun kashe dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya guda biyu dake aiki a arewacin kasar lokacin da suka kai musu hari.

Wasu daga cikin dakaru dake aiki a kasar Mali
Wasu daga cikin dakaru dake aiki a kasar Mali defense.gouv.fr/operations
Talla

Hukumar dake kula da aikin samar da zaman lafiyar tace Yan bindigar sun kaiwa dakarun hari ne lokacin da suke tafiya tsakanin garuruwan Tessalit zuwa Gao ranar asabar da yamma.

Sanarwar hukumar tace motocin tawagar ta tsaya ne lokacin da Yan bindigar suka bude musu wuta a kusa da kauyen Tarkint kafin sojin su mayar ad martini.

Shugaban hukumar samar da zaman lafiyar Mahamat Saleh Annadif yayi Allah wadai da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI