Najeriya

Mayakan ISWAP sun hallaka mutane 6 a Manguno

Some Nigerian Soldiers. Nigeria Defence Headquarters denies burying soldiers killed by Boko Haram in secret graves. [REUTERS/Warren Strobel]
Some Nigerian Soldiers. Nigeria Defence Headquarters denies burying soldiers killed by Boko Haram in secret graves. [REUTERS/Warren Strobel] REUTERS/Warren Strobel

Mayakan dake ikrarin jihadi na kungiyar Isis a yammacin Afrika (ISWAP) a jiya assabar sun hallaka mutane 6, a wani hari da suka kai kan wani barikin soji dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda majiyar tsaro da shaidu suka tabbatar.

Talla

Mayakan na 'ISWAP sun gwabza fada da sojojin Najeriya dake samun goyon bayan mayakan sa kai dake taimakawa gwamnati, bayan abkuwar harin da a garin Monguno dake daf da tafkin Tchad.

Sojoji 2 mayakin sa kai guda da kuma wasu fararen hula 3 ne suka kwanta dama a karkashin harin, da suka dau tsawo sa’o’i 2 su na gwabzawa, da mayakan na Iswap, kamar yadda Bukar Ari, daya daga cikin mayakan dake taimakawa sojoji fada da kungiyoyin mayakan a Najeriya ya sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.