Nijar

Niger ta bayyana takaicinta kan zargin sojinta da kisa fararen hula a Mali

Ministan harakokin wajen Nijar Kalla Hakurau
Ministan harakokin wajen Nijar Kalla Hakurau JOHN THYS / AFP

Kasar Jamhuriyar Nijer ta bayyana matuka bacin ranta dangane da zargin da ake yi kasar suka aikata a yankunan kan iyakar kasar da Mali, inda kasar ta ce a shirye take kungiyoyin kasashen duniya su gudanar da binciken tabbatar da gaskiya, kamar yadda ministan harakokin wajenta kalla hakurau ya sanar .

Talla

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch.

da kuma rundunar samar da zaman lafiya ta MDD a kasar Mali Munisma ne suka zargi sojojin kasashen Mali da jamhuriyar ta Nijer, da kashe fararen hula sama da 100 a wani yankin kan iyaka dake cikin kasar Mali a kokarinsu na fada da yan ta’adda masu ikararin jihadi a yankin.

A firarsa da radiyo faransa Ministan harakokin wajen kasar ta jamhuriyar Nijer kalla Hakurau, ya musanta zargin, da ya danganta da zama abin takaici da wasu yan barandan yan ta’adda su ka kirkira domin bata wa sojojin na Nijer suna.

Har ila yau, minista kalla ya bukaci a gabatar da shaidu ko kuma kabarin da aka binne mutanen.

Ya kara da cewa yan ta’adda na iya shigar burtu da kayan sojin Nijer su aikata ta’asa, da nufin bakanta sojojin kasar a idon duniya.

Don haka Nijer bata da wata damuwa, tana ma gayyatar kungiyoyin duniya da su gudanar da bincike domin tabbatar da kaskiya a cikin lamarin.

su ba wata damuwa idan ana bukatar a gidanar da bincike

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI