Nigeria

'Yan Boko Haram sun halaka mutane 38 a Goni Usmanti

Wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram a Najeriya
Wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram a Najeriya Defencepost

Mayakan Boko Haram sun kashe fararen hula akalla 38 a wani kazamin harin da suka kai kauyen Goni Usmanti dake da nisan kilometa kusan 60 da Mungono dake Jihar Barno, mako guda bayan kashe mutane sama da 80 a Gubio dake Jihar.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa na Afp ya ruwaito cewar mayakan sun kai harin ne jiya asabar da safe inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi da kuma cinnawa motar dake dauke da jama’a wuta.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da wasu maharan kuma suka kai hari Manguno amma sojin Najeriya suka yi nasarar murkushe su.

Rahotanni sun ce mutane 15 sun mutu a fafatawar da akayi tsakanin mayakan da sojin Najeriya a Manguno, kuma cikin su harda sojoji 9 kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito.

Matsallar tsaro na ci gaba da ciwa jama'a tuwo a kwariya,musaman arewacin Najeriya,yankin da yan Boko Haram suka yawaita kai hare-hare a dan tsakanin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.