Duniya

Amurka zata gana da kasashen Turai dangane da batun Falesdinu

Yau ake saran ministocin kungiyar kasashen Turai zasu gudanar da wani taro ta bidiyo tare da takwaran su na Amurka Mike Pompeo saboda barakar dake tsakanin su kan mamayar da Isra’ila ke yiwa yankunan Falasdinawa da baraka kan hukumomin Duniya da kuma yadda zasu tunkari kasar China.

Yankunan zirin Gaza
Yankunan zirin Gaza
Talla

Ana saran ministocin zasu bayyana wa Pompeo adawar kasashen su da shirin mamaye karin yankunan Falasdinawa da Isra’ila ke yi wanda suka ce ya sabawa dokokin duniya.

A makon jiya ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ziyarci Isra’ila inda ya shaidawa Firaminisra Benjamin Netanyahu cewar kasashen Turai basa goyan bayan kasar ga duk wani shiri na mamaye yankunan Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI