Ana fargabar mutuwar Sojin Mali 40 a wani harin 'yan Bindiga
Rahotanni daga kasar Mali sun ce akalla sojojin kasar 40 suka mutu ko kuma suka bata lokacin da 'yan bindiga suka kai wa tawagar motocin hari a tsakiyar kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wani babban jami’in soji ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar mayakan sun budewa motoci 12 dake dauke da sojojin wuta ne a Bouka Were dake da nisan kilomita 100 daga iyakar Maurtania jiya lahadi.
Majiyar tace sojoji 64 ke cikin tawagar lokacin da aka kai musu hari, kuma ya zuwa yanzu 20 kawai aka samu da ran su, yayin da babu wanda yaki duriyar sauran.
Ya zuwa yanzu dai an kaddamar da bincike ko za’a sami wasu daga cikin sojojin da ran su.
Wannan na daga cikin hare hare na baya bayan nan da Yan bindigar dake ikrarin jihadi suka kaddamar kan dakarun sojin kasar tun bayan daukar makamai a shekarar 2012.
Ko a ranar asabar Yan bindigar sun kasha sojojin Masar guda 2 dake aikin samar da zaman lafiya a karkashin Majalisar Dinkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu