Faransa ta soki matakin Turkiya a Libya
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Faransa ta soki matakan da Turkiya ke dauka a kasar Libya wajen taimakawa gwamnatin hadin kan kasar a matsayin abinda ba zata amince da shi ba, inda tace ya sabawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya.
Faransa ta nuna bacin ran ta da yadda Turkiya ta tura jiragen ruwan yaki guda 7 gabar ruwan Tripoli domin hana Janar Khalifa Haftar yunkurin sa na karbe iko da birnin.
Bayan ta dade tana kin amincewa da zargin da ake mata cewar tana goyawa Janar Khalifa Haftar baya, faransa tace ba zata zuba ido tana kallon Turkiya na yin abinda ta ga dama a Libyar ba.
Faransa a wata wasika mai dauke da sanya hannun fadar Shugaban kasar ta mai Allah wadai ga shirin Turkiya na shiga yakin Libya da nufin kawo yamuci ga duk wani shirin na sassanta bangarori dake fada da juna.
A cikin wannan mako dake karewa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya samu tattaunawa da Shugaban Amurka,inda ake kuma sa ran manyan kasashen za su samu tattaanawa da kungiyar Nato a Kai..
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu