Afrika

Najeriya na bin kasashen Togo,Nijar da Benin sama da naira biliyan 32

Kamfanin samar da hasken wutar lantarki na NEPA a Najeriya
Kamfanin samar da hasken wutar lantarki na NEPA a Najeriya Daily Trsut

Gwamnatin Najeriya tace tana bin kasashen Togo da Nijar da Jamhuriyar Benin sama da naira biliyan 32 kudin wutar lantarki da suka rike mata na shekarar 2019.

Talla

Hukumar dake samar da wutar tace ana bin kamfanin wutar Nijar sama da naira biyan 12 a shekarar da ta gabata, sai kamfanin Togo dake samarwa Benin da Togo wuta da ake bi sama ad naira biliyan 19.

Duk da gazawa wajen samarwa jama’ar kasar ta wutar, Najeriya na baiwa kasashen dake makoftaka da ita wutar akai akai.

Kungiyoyi da dama ne a kasar ta Najeriya suka bayyana damuwa da kuma bukatar ganin gwamnati ta taka rawar da ta dace don kawo karshen wannan matsalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI