Afrika

Shugaban Mali ya shirya domin ganawa da masu bore

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita yace a shirye yake ya gana da tawagar yan adawar kasar dake bukatar ganin ya sauka daga mukamin sa domin tattauna matsalolin da suka addabi kasar ta Mali.

Masu zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali
Masu zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali REUTERS/Matthieu Rosier
Talla

Ibrahim Boubacar Keita yace kofar sa a bude take domin tattaunawa da yan adawan duk lokacin da suke bukata a kasar dake cigaba da fuskantar tashin hankali da hare haren yan bindiga.

A farkon wannan wata dubban mutane sun gudanar da zanga zangar a Bamako inda suka bukaci shugaban ya sauka daga mukamin sa saboda gazawa wajen kare lafiyar jama’ar kasar.

Daga cikin masu adawa da Shugaban kasar ta Mali akwai babban Imam Mahmoud Dicko, dake shugabantar hadin gwuiwar kungiyoyi da aka sani da FSD,wanda ya bayyana cewa za su cigaba da zanga-zanga har sai Shugaban ya sauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI