Za'a rantsar da sabon shugaban kasar Burundi bayan mutuwar Nkurunziza

Zababben shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye
Zababben shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye AFP

Gwamnatin Burundi ta ce a ranar Alhamis mai zuwa za’a rantsar da zababben shugaban kasa Evariste Ndashimiye kamar yadda kotun koli ta bada umurni domin maye gurbin shugaba Pierre Nkurinziza da ya mutu a makon jiya.

Talla

Tuni ma’aikatar harkokin wajen kasar ta aike da takardun gayyata ga jakadu da jami’an diflomasiya domin halartar bikin shan rantsuwar da za’ayi a Gitega, babban birnin kasar.

Ndashimiye mai shekaru 52, tsohon Janar ne na sojin kasar kana kuma tsohon dan tawaye ne daga bangaren Yan kabilar Hutu a rikicin kasar.

A zaben da ya gudana, Ndashimiye ya samu kusan kashi 69 na kuri’un da aka kada, abinda ya bashi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.