Buhari ya baiwa mutanen Katsina hakuri
Wallafawa ranar:
Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya bukaci jama’ar Jihar Katsina da suyi hakuri domin gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen yaki da yan bindigar da suka addabe su, yayin da ya jajantawa wadanda suka rasa yan uwan su.
Wata sanarwa da Garba Shehu, mai Magana da yawun Shugaban Buhari ya rabawa manema labarai, tace fita kan tituna ana zanga zanga da yan Jihar suka yi zai dauke hankalin jami’an tsaro daga yakin da suka kaddamar kan Yan ta’adda, inda ya bukaci al’ummar Jihar da su cigaba da goyawa sojoji baya domin samun nasara kamar yadda suka samu a shekarun baya.
Buhari yace tuni jami’an tsaro suka gano maboyar Yan bindigar a dajin dake Arewa Maso Yammacin kasar kuma zasu kawar da su daga ciki, ganin yadda aka inganta bincike da leken asisri, yayin da jiragen yaki na kai hare hare har cikin dare.
A yau mazauna Jihar Katsina sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin ran su da yadda Yan bindigar ke cigaba da hallaka su ba tare da kaukautawa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu