DR Congo-Ebola

Ebola ta kashe mutane 11 a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Wata gawa da Ebola ta kashe lokacin binneta a yankin Beni na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Wata gawa da Ebola ta kashe lokacin binneta a yankin Beni na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Hukumomin Jamhuriyar demokradiyyar Congo sun ce sun samu mutane 17 dauke da cutar Ebola, yayin da wasu 11 kuma suka mutu a Yankin Equateur.

Talla

A makon jiya hukumomin lafiyar kasar sun ce an samu mutane 12 da suka kamu da cutar, yayin da kasar ke yaki da cutar wadda ta kasha mutane sama da 6,000 kafin barkewar coronavirus da ta hallaka mutane 112 a kasar.

Hukumar yaki da cututtukar kasar tace yanzu haka suna dauke da mutane 14 da aka tabbatar sun kamu da cutar daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.