Bakonmu a Yau

Kwamishinar Mata a Kaduna Hajiya Hafsa Baba kan samun laifukan Fyade 717 cikin watanni 5

Sauti 03:40
Yadda mata kan fuskanci mafi munin tashin hankali bayan yi musu fyade.
Yadda mata kan fuskanci mafi munin tashin hankali bayan yi musu fyade. guardian.ng

Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya Muhammadu Adamu ya ce a cikin watanni 5 da suka gabata an samu mutane 717 da suka yiwa mata fyade a kasar, matakin dake dada nuna yadda ake cin zarafin mata a kasar.

Talla

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin, Sufeto Janar Adamu yace yanzu haka rundunar sa na tsare da mutane 799 da ake zargi da aikata wannan laifi daga cikin laifuffuka 631 da aka gabatar musu kuma suka mika kotuna.

Dangane da wannan matsala, mun tattauna da kwamishiniyar kula da harkokin mata a Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, kuma ga tsokacin da tayi akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.