Burundi

Sabon shugaban kasar Burundi Evariste Ndashimiye zai sha rantsuwar fara aiki

Zababben shugaban na Burundi Evariste Ndashimiye.
Zababben shugaban na Burundi Evariste Ndashimiye. Tchandrou NITANGA / AFP

Gwamnatin Burundi ta ce a ranar alhamis mai zuwa za’a rantsar da zababben shugaban kasa Evariste Ndashimiye kamar yadda kotun koli ta bada umurni domin maye gurbin shugaba Pierre Nkurinziza da ya mutu a makon jiya.

Talla

Tuni ma’aikatar harkokin wajen kasar ta aike da takardun gayyata ga jakadu da jami’an diflomasiya domin halartar bikin shan rantsuwar da za’ayi a Gitega, babban birnin kasar.

Ndashimiye mai shekaru 52, tsohon Janar ne na sojin kasar kana kuma tsohon dan tawaye ne daga bangaren 'yan kabilar Hutu a rikicin kasar.

Yayin zaben kasar da ya gudana cikin watan jiya, Ndashimiye ya samu kusan kashi 69 na kuri’un da aka kada, abinda ya bashi nasara.

Tun a makon jiya ne dai kotun kundin tsarin mulkin kasar ta bukaci gaggauta rantsar da zababben shugaban biyo bayan mutuwar shugaba Pierre Nkurunziza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.