Saudiya

Wasu na ganin cewa ya dace a soke aikin hajji bana

Masallacin Ka'aba na Saudiya
Masallacin Ka'aba na Saudiya REUTERS

A yayin da cutar coronavirus ke cigaba da ‘karuwa a sassan duniya masu lura da al’ammura a Saudiyya sun ce ya kamata kasar ta rage yawan mahajjata ko ta soke aikin hajjin bana, matakin da zata dauka karon farko a tarihinta na gudanar da ayyukan hajji.

Talla

Kasashen musulmai sun matsawa Saudiyya ta sanar da matsayarta a kan aikin hajjin bana, bayan shafe tsawon lokaci tana nazari a kan matakin, a karshen watan yuli mai zuwa ya kamata a fara gudanar da hajji kamar yadda aka tsara.

Sai dai a yayin da Saudiya ke cigaba da tafka muhawara dan shawo kan matsalolin tattalin arziki da na siyasa dake addabar ta, lokaci na dada kurewa wajen tsara yadda ya kamata a gudanar da daya daga cikin taro mafi girma a fadin duniya da aka saba gudanarwa kowacce shekara.

Ana hasashen da wuya a gudanar da aikin hajjin bana bayanda a karshen watan maris da ya gabata ne hukumomi suka shawarci musulmai a fadin duniya da su dakatar da shirin ganin yadda annobar coronavirus tayi ta yaduwa tamkar wutar daji.

Wani jami’in Saudiyya ya shaidawa kamfanin dillancin labaran faransa AFP cewa nan ba da jimawa ba za’a cimma matsaya kuma ba tare da an bata lokaci ba, za’a sanar.

Tuni dai Kasashen dake da mafi yawan alummar musulmi irin su Indonesia, Malaysia, Senegal da kuma Singapore suka sanar da matakinsu na janyewa daga aikin hajjin bana, sauran kasashen kuwa sun ce suna dakon sanarwar Saudiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.