Nijar

Yan Boko Haram sun kai hari garin Tumour

Wasu daga cikin sojoji dake fada da mayakan kungiyar Boko Haram
Wasu daga cikin sojoji dake fada da mayakan kungiyar Boko Haram AFP

A cikin daren jiya, mayakan Boko Haram su kai hari garin Tumour dake da nisan kilometa 70 da garin Diffa.A wannan hari, yan kungiyar ta Boko Haram sun yi awon gaba da kusan mutane 20 da suka hada da mata da yara.

Talla

Da samun labarin wannan hari,sojojin Nijar sun samu nasarar fatatakar mayakan Boko Haram yan lokuta da fitar su daga garin na Tumour.

Yankin na Diffa ya kasance wani yanki da yan Boko Haram duk da kokarin hukumomin Nijar ke cag aba da cin karnen su ba babaka.

Wasu daga cikin kungiyoyi na ci gaba da kira ga hukumomin kasashen Sahel na ganin sun hada karfi wajen yakar mayakan kungiyar ta Boko Haram kamar yada kasar Cadi ta dau mataki a baya na shiga kasashen Nijar, Najeriya don yakar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI