Afrika

Yau ake bikin ranar yaran Afrika ta Duniya

16 ga watan Yuni, rana ce da kungiyar hadin kan kasashen Afirka OUA a wancan lokaci ta ayyana a matsayin ranar yaran Afirka ta duniya bisa amincewar Majalisar Dinkin Duniya, tun a shekarar 1991, inda ake nazari kan halin da yaran ke ciki masamman harkokin iliminsu.

Wasu kananan yara a garin Maiduguri na jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya.
Wasu kananan yara a garin Maiduguri na jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya. Reuters/Kieran Guilbert
Talla

Kungiyar hadin kan kasashen Afirka a wancan lokaci OUA, da yanzu aka sauyawa suna zuwa AU, ta ware kowace ranar 16 ga Yuni, domin tunawa da jajircewar da wasu dalibai bakaken fata daga Soweto na Afirka ta Kudu suka nuna a shekarar 1976.

Kusan dalibai dubu 10 suka gudanar da zanga-zanga a titunan Soweto wancan lokaci, domin nuna adawarsu, kan rashin ingancin harkokin iliminsu, dangane da wata doka dake ban-banta dalibai bakar fata da takwarorinsu farar fata.

Abin takaici danage da wannan zanga-zangar ta lumana na tsawon makonni biyu, shine yadda jami’an tsaro suka rika harbi, inda suka kashe kimanin sama da dalibar 100, tare da raunata sama da dubu daya.

Ranar Yara ta Afirka kuma wata dama ce ta wayar da kan jama'a kan bukatar ci gaba da inganta ilimin yaran da ke rayuwa a duk fadin Afirka. Wata bukata ce da har yanzu take da yawa a yau. Daga cikin yara miliyan 57 na makarantar firamare a halin yanzu ba su zuwa makaranta a duniya, sama da rabi suna daga yankin Saharar Afirka.

A shekarar 1991, kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta ware ranar tunawa da daliban bakar fata wanda Majalisar Dinkin Duniya ta goyi ba, sai dai bukin na bana na zuwa ne adai-dai lokacin kasashen duniya ke fama da annobar koronavirus, wanda ta tilastawa dalibai firamare kadai kimanin miliyan 57 zaman gida akasarinsu daga yankin kudu da Saharan Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI