Afrika-Amurka

Afrika ta matsa lambar ganin an binciki batun cin zarafin bakar fata a Amurka

Wasu masu zanga-zangar kyamar nuna wariya a Amurka.
Wasu masu zanga-zangar kyamar nuna wariya a Amurka. Dave Chan / AFP

Kasashen Afirka na matsin lamba ga hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ta kaddamar da bincike kan yadda ake nuna wariyar jinsi a Amurka da kuma yadda 'yan Sandan kasar ke cin zarafin bakaken fata.

Talla

Batun na daga cikin abinda taron hukumar zai tattauna akai yau a Geneva, sakamakon kisan gillar da aka yiwa George Floyd da kuma abinda ya biyo baya.

Daftarin da kasashen Afirka suka gabatar domin tattaunawa akai ya yi ala wadai da yadda har yanzu ake nunawa bakar fata kyama a Amurka da kuma yadda 'yan Sanda ke takura musu.

Daftarin ya bukaci kafa wata Hukumar bincike mai zaman kan ta, kamar irin wanda akayi a rikicin Syria.

Akwai dai tarin hujjoji da ke nuna yadda bakar fata kan fuskanci tsananin matsin lamba a Amurka duk kuwa da kasancewar galibinsu 'yan asalin kasar.

A baya-bayan nan dai mabanbantan faya-fayan bidiyo sun fita wadanda ke nuna yadda 'yan sandan na Amurka ke cin zarafin bakar fata, tare da tirsasa musu amsa laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.