Najeriya-Chadi

Chadi na barar wutar lantarki daga Najeriya

Najeriya na bai wa kasashen Afrika makwabta wutar lantarki
Najeriya na bai wa kasashen Afrika makwabta wutar lantarki REUTERS/Christian Hartmann

Gwamnatin Kasar Chadi ta bukaci Najeriya da ta taimaka mata wajen bata hasken wutar lantarki kamar yadda take bai wa wasu kasashe da ke makwabtaka da ita.

Talla

Jakadan Chadi a Najeriya Abakar Saleh Chachaimi ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci Ministan Samar da Wutar Lantarkin kasar, Saleh Mamman, inda yake cewa bukatarsu ta gaggawa ce saboda muhimmancin wutar.

Mamman ya yaba da karbar bukatar ta Chadi daga hannun jakadan wanda ya ce, zai taimaka wajen inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Mamman ya ce, bukatar ta Chadi na zuwa ne a wani lokaci da Najeriya ke fafutukar inganta harkar samar da wutar, inda ya shaida wa jakadan cewa,  Najeriya za ta yi nazari kan bukatar da zummar taimaka wa kasar.

Ministan ya shaida wa jakadan na Chadi cewa, yanzu haka Najeriya na samar wa Jamhuriyar Nijar da Benin wutar lantarki bayan sun sanya hannu a wata yarjejeniya shekaru da dama da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.