Najeriya

Jami'an Kwastam sun kona dimbin kayayyaki a Seme

A Najeriya Jami’an Kwastam na shi’ar Seme kan iyakar kasar da jamhuriyar Benin, sun kona tarin kayaki da aka yi kokarin shigo da su kasar ba bisa ka’ida ba a ranar Laraba da ta gabata.

Lokacin da ake kone tarin kayaki a Seme
Lokacin da ake kone tarin kayaki a Seme RFI Hausa
Talla

Bisa rakiyar Shugabanin rundononin tsaron yankin Shugaban shi'ar Seme kwantroller CD Wada ne ya jagoranci bikin kone tarin kayakin da jami'an sa suka kama da kuma akai yi kokarin shigo da su ta bayan fage.

Shugaban kwastam shi'ar seme ya samu tattaunawa da shugabanin al'umat,inda yayi amfani da wannan dama don nuna musu irin illar dake cikin ayyukan fasa kwabri, banda haka ya nemi shugabanin sun kawo nasu goyan baya don kawar da da haka tarade samar da mafita cikin dan karamin lokaci.

Akala an cinawa kayaki na kusan milyan 168,383.511.00 na Naira wuta a garin na Seme dake kan iyaka da Jamhuriyar Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI