Bayan dogon hutu da shirin ya tafi sakamakon annobar coronavirus wadda ta tilasta dakatar da ilahirin wasanni a Duniya, to awannan mako shirin ya dawo yadda aka saba jin sa,A karshen mako aka koma gasar La liga ta kasar Spain, gasa ta biyu mafi girma a nahiyar turai bayan gasar pirimiya, kuma hakan ne yasa shirin na wannan mako zai maida hankali kan dawowar gasar da kuma kalu balen dake tattare da kungiyoyi da kuma su kansu yan wasa, lura da dogon hutun da suka share ba tare da atisaye ba.